Gidauniyar ELOY Foundation tare da hadin gwiwar kungiyar MATA Network sun horas da mata 100 dari akan hanyoyi dogaro da kai a jihar Kano.
Shugaban gidauniyar ta ELOY Foundation, Tewa Onasanya, ta ce munifar bada horarswar shine a nunawa mata hanyoyin dogaro da kai ta yacce zasu sami nasara a rayuwar su.
A nata bangaran shugaban kungiyar MATA Network, Yasmin Obadaki, ta bawa matan da suka samu horan shawarwari akan amfanin da dabarun zamani ya yin gudanar da kasuwancin su.
Ya yin taron bada horon an kawo labarai na mata ‘yan kasuwa wadan da suka sami nasara a rayuwa sakamakon bada himma da jajirciwar su a lokacin da suka fara sana’o’in dogaro dai, duk dai da niyar zabarar da matan akan amfani da damarmakin da suke hannun su.












































