Manchester City Ta Yiwa Real Madrid Raga-Raga A Wasan Kusa Da Na Karshe.

Kungiyar kwallon kafa ta Man City ta samu tikitin kaiwa ga wasan karshe a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai ta shekarar 2023, bayan da ta yi wa Real Madrid dukan kawo wuka.

Awasan farko da aka buga tsakanin manyan kungiyoyin 2, an tashi 1-1, yayin da akaro na biyu Man City ta jefa kwallaye 4 babu ko daya a filin wasa na Etihad dake England.

Ayanzu haka wasan karshe zai kasance tsakanin Manchester City da Inter Milan a birnin Istanbul na kasar Turkiya

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here