NNPP Na Neman a Janye Takardar Shaidar Cin Zaben Doguwa a Kotu.

Rikici na cigaba da dumama kan shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Hon. Alhassan Ado Doguwa a yayin da jam’iyyar NNPP ta bukaci a janye masa takardar shaidar cin zabe da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ba shi.

Idan za a iya tunawa, Kotun sauraron kararrakin zaben ‘yan majalisun tarayya ta amince da bukatar jam’iyyar NNPP na like sammacin korafin da sukewa Doguwa a sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa.

An ayyana Doguwa a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar sa ta Doguwa da Tudun-Wada da kuri’u Dubu 41,573 inda ya kayar da abokin hamayyarsa Yusahu Salisu na jam’iyyar NNPP wanda ya samu kuri’u 34,831.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa, sakamakon rashin gamsuwa da sakamakon zaben, jam’iyyar NNPP ta shigar da kara a gaban kotun sauraron kararrakin zaben ‘yan majalisar dokokin da ke zamanta a Kano, a ranar Larabar da ta gabata, inda ta bukaci kotun da ta yi watsi da ayyana Doguwa a matsayin wanda ya lashe zaben.

A cikin karar da lauyansu, Bashir Mohammad, NNPP da dan takarar suka shigar, ya bayyana cewa zaben da ya samar da Doguwa a matsayin wanda ya lashe zaben ya kasance da gagarumin magudi wanda jami’in zabe na mazabar suka tabbatar.

Masu shigar da kara sun koka da yadda Doguwa ya yi facaka a lokacin zaben, inda jami’in da ya bayyana sakamakon ya tabbatar da cewa an tilasta masa ne ya bayyana Doguwa wanda ya lashe zaben.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here