Gwamna Ganduje ze yi karar jadirar Sahara reporters bayan fitar rahoton EFCC.

Ganduje sad
Ganduje sad

Gwamnatin Kano ta yi Allah-wadai da kakkausar murya ga wata kafar yada labaran yanar gizo ta Sahara Reporters ta yi na cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na daya daga cikin gwamnoni uku da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa ta’annati ke zargin su da taskace kudaden sata a gidajensu.

Sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai, Malam Muhammad Garba ya gabatar ta nuna cewa yayin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ba ta fadi sunayen gwamnonin ba, Sahara Reporters gaba-gadi ta ci gaba da yada wannan maganar ta karya.

Jaridar SOLACEBASE ta rawaito cewa lamarin ya zama abin tattaunawa a Kano tun bayan da aka fidda rahotannin a ranar Juma’a, inda wani fitaccen mai sharhi a gidan rediyon jihar ya bukaci Ganduje da ya tabbatar da sahihancin abun da Sahara Reporters ta ambata ko kuma ya karyata.

A cewar sanarwar, rahoton ba shi da wani tushe, kawai dai hasashe ne na mawallafa a wani yunkuri na bata sunan gwamnan da gangan.

“Malam Garba ya yi nuni da cewa Gwamna Ganduje baida wasu biliyoyin Naira da ya boye a cikin gidaje da akayi zargin zeyi biyan albashin ma’aikata dasu” inji sanarwar.

“Kwamishanan ya kara da cewa Kano na daya daga cikin jahohin tarayya da suke biyan albashin ma’aikatanta akai-akai, duk da cewa a lokacin fitar da rahoton karyar da Sahara Reporters ta fitar, an fara saka albashin watan Oktoba.

Kwamishinan labaran ya yi kira dasu janye labarin tare da neman afuwa ba tare da bata lokaci ba, wanda kin bin wannan umarnin gwamnatin jihar, zai janyo daukar matakin shari’a akan su’’.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here