Zulum ya umarci mai ba da shawara Kan harkokin shari’a ta sanya ido kan ma’aikatar shari’a, har zuwa lokacin da za a nada sabon kwamishina

Borno 1
Borno 1

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya umarci mai ba shi shawara ta musamman kan harkokin shari’a, Barista Hauwa Abubakar da ta sa ido a ma’aikatar shari’a ta jihar, har sai an nada babban lauyan gwamnati Kuma kwamishinan shari’a.

Sakataren gwamnatin jihar Borno ne ya isar da umarnin gwamnan a cikin wata wasika mai kwanan wata 11 ga watan Agustan Shekarar da muke ciki ta 2022, wacce aka aike wa mai ba shi shawarar ta musamman.


Wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yada labarai Malam Isa Gusau ya fitar a ranar Asabar, ta ce umarnin kula da ma’aikatar ya biyo bayan murabus din tsohon babban lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari’a, Barista Kaka Shehu Lawan, wanda ya zama dan takarar Sanatan Borno ta tsakiya, a jam’iyyar APC.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here