Dan takarar Sanatan Jigawa ta tsakiya a Jam’iyyar APC Alhaji Tijjani Ibrahim Kiyawa ya rasu.
Tijjani Ibrahim Kiyawa, wanda tsohon dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kiyawa da Dutse a majalisar wakilan tarayya ya rasu ne a wani asibitin kasar China ranar Asabar.
Rahotanni sun ce da farko an kwantar da shi a wani asibiti dake Abuja sakamakon rashin lafiyar amma daga bisani an garzaya da shi kasar China domin ci gaba da kula da lafiyarsa.
Sakon ta’aziyyar da mai baiwa Gwamna Muhammad Badaru Abubakar, shawara na musamman kan harkokin yada labarai Habibu Nuhu Kila ya fitar a ranar Lahadi, ya tabbatar da rasuwar dan takarar Sanatan a zaben 2023 mai zuwa.
A cewar sanarwar, gwamnan ya ce rasuwar Tijjani Ibrahim Kiyawa babban rashi ne ba ga iyalansa kadai ba har ma da al’ummar musulmi baki daya.

“Ya bayyana marigayi Alhaji Tijjani Ibrahim Kiyawa a matsayin dan siyasa mai aminci da kuma rikon amana wanda ya bayar da gudunmawa sosai ga ci gaban siyasar kasar, na ” in ji sanarwar.
‘’Gwamna Badaru ya roki Allah Madaukakin Sarki da ya ba shi hutu na har abada, ya kuma ba iyalansa hakurin jure rashin.












































