ENaira: CBN da Fintech Foundry zasu tallafawa Kamfanoni 10 a Najeriya

Judges at the Semi Final Pitching of the eNaira Hackathon 2022 in Lagos on Saturday Aug. 13 2022. 750x430 1
Judges at the Semi Final Pitching of the eNaira Hackathon 2022 in Lagos on Saturday Aug. 13 2022. 750x430 1

Kamfanin Afirka Fintech Foundry (AFF) ya ce ya hada kai da babban bankin Kasa (CBN) don tallafawa kamfanoni 10 da za su fara aikin, gudanar da tsarin eNaira a kasar.

Shugaban kamfanin, Mista Daniel Awe, ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) ranar Asabar a Legas.

Awe ya ce Kamfanoni da zasu fara guda 10, na kirkire-kirkire, ne da na ’yan kasuwa, suna cikin Kamfanoni sama da dubu 5 da suka fara rajista da tsarin eNaira Hackathon.


Ya ce akwai bukatar a kara amfani da kudin eNaira a kasar nan, saboda ana sa ran zai inganta hada-hadar kudi, sannan zai tallafawa tsarin tattalin arziki na dijital da Kuma inganta harkokin tattalin arziki.

“CBN ya bullo da tsarin eNaira ne tun a shekarar 2021.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here