Yan sanda sun kama shahararren mawakin Najeriya wanda aka fi sani da Ice Prince a Legas saboda dukan jami’in dan sanda.
Rahotanni sun ce misalin karfe 3 na daren ranar Juma’a ne yan sandan suka tare mawakin saboda yana tuki ba tare da lamba ba.
Ice Prince wanda da farko ya yarda zai bi jami’in dan sandan su tafi caji ofis nan take, ya sace dan sandan a cikin motarsa, ya masa duka, kuma ya yi barazanar zai jefa shi cikin kududufi.
Mai magana da yawun yan sandan Jihar Legas SP Benjamin Hundeyin, a shafinsa na Twitter ya ce an kama Ice Prince kuma za a gurfanar da shi a kotu yau.
A cewar Hundeyin: “Misalin karfe 3 na dare ne aka tsayar da @Iceprincezamani saboda tuki ba bu lasisi. Ya yarda a tafi da shi caji ofis.
“Daga baya, ya sace dan sandan da ke cikin motarsa, ya masa duka, kuma ya yi barazanar zai jefa shi cikin rafi.
“An kama shi kuma za a gurfanar da shi a yau.”













































