Rikicin Sudan: Daliban Jigawa 41 Sun Iso Birnin Dutse.

Kimanin ‘yan asalin jihar Jigawa 107 da ke karatun likitanci a kasar Sudan, akalla 41 ne suka dawo da jihar lami lafiya a yau bayan kwaso su da gwamnatin tarayya ta yi daga kasar da ke fama da rikici.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa daliban sun isa filin jirgin saman Dutse da karfe 1.55 na rana.

Kamfanin dillancin labarai NAN ya kuma rawaito cewa, tashar jirgin ta ga dimbin iyayen da suka fito, da kuma ‘yan uwan ​​wadanda suka dawo, suna maraba da su cikin farin ciki.

Dokta Abubakar Sani, Babban Sakataren Hukumar Ilimin Musulunci ta Jihar Jigawa wanda ya karbi bakuncin wadanda suka dawo a madadin Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dakta Lawan Danzomo, ya bayyana farin cikinsa da cewa babu daya daga cikin daliban da ya samu rauni ko kuma ya yi rashin lafiya sakamakon rikicin da ke faruwa a Sudan.

“Mun gode wa Allah Madaukakin Sarki da ya cece ku, kuma babu daya daga cikinku da ya samu wani rauni ko ya yi rashin lafiya.

“Don haka dole ne ku yaba da kokarin su, ciki har da zababben gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, bisa kokarinsu da kuma damuwarsu na dawo da ku gida lafiya.

Malam Abdullahi Yunusa, Babban Darakta Janar na Hukumar Kula da Ilimi ta Jihar Jigawa (SEMU) ya shawarci wadanda suka dawo gida da kada suyi sanya wajan maida hankali ganin sun kammala karatunsu.

Yunusa ya bukace su da su ci gaba da karanta littattafansu a gida har zuwa lokacin da gwamnati za ta yanke hukunci kan makomar karatunsu.

“Ba ku ne farkon da kuka fuskanci irin wannan ba, kuma ɗalibai a Ukraine da Rasha sun fuskanci irin wannan matsala.

A nasa bangaren, Sakataren zartarwa na Hukumar bayar da tallafin karatu ta jiha Alhaji Sa’idu Magaji, ya ce kokarin da gwamnatin jihar ke yi na ganin daliban sun koma gida lafiya, ya bi hakkin da tsarin mulki ya dora musu na kare rayuka da dukiyoyinsu.

Magaji ya bayyana cewa daukacin dalibai 107 da aka kwaso daga kasar Sudan, sun isa filin jirgin saman Dr Nnamdi Azikwe, Abuja lami lafiya.

“Mun karbi 41 daga cikin 107 na dalibanmu da ke karatu a Sudan, Sauran sunanan ana duba su a filin jirgin Abuja.

Kqmfanin dillacin labaran najeriya ya kuma rawaito cewa wadanda suka dawo suna cike da murna, an baiwa kowannensu Naira 5,000 a matsayin kudin jigila zuwa gidajensu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here