Jam’iyyar NNPP ta dakatar da sakataren gwamnatin Kano, Kwamishina

nnpp logo new 588x430

Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano, Hashimu Suleiman Dungurawa ya ce sun dakatar da Dr Baffa Bichi da kuma kwamishinan sufuri na jihar, Muhammad Diggol bisa zargin ‘keta alfarmar jagoranci da ta gwamnati’.

Dungurawa ya ce dakatarwar za ta yi aiki har sai sun gama bincike a kan su.

“Jam’iyyar ba za ta lamunci ayyukan da ke lalata shugabancinta da tsarinta ba. Bayan mun samu wasikun korafe-korafe daga unguwanninsu, da kuma tabbatar da zargin da shugabannin yankin suka yi mana, ba mu da wani zabi illa daukar wannan muhimmin mataki,” in ji Dungurawa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here