HALIN KA, SABULUN WANKAN KA: Shin a Haka Yan Najeriya Zasu Dauwama???

IMG 20220425 WA0171
IMG 20220425 WA0171

Aminu Bala Madobi

Wato a Najeriya idan kana son ka gane cewa mu Talakawan Nigeria, Allah Yaa zaɓa mana shugabanni ne daidai damu, ba zaka sha wahala ba! kasancewar Duk wani masallaci, za kaga an yima Amplifier keji, da rodikan karfe an saka makulli an rufe.
Duk wani masallaci zaka ga an yima Agogo keji an saka makulli an rufe, Saboda gudun Sharrin Talakan Nigeria. Generator wanda yake baiwa masallacin wutar latirin, sai an masa cikakkiyar adanawa, tare da saka masa kacha, asa makulli a kulle. A wasu guraren Saboda gudun sharrin Talakan Nigeria, a hakan duk ba’a tsira ba ana sa ran za’a iya sacewa!

A mafi yawan Masallatai, da zaran ka cire takalmin ka masu kyau, ka barshi a qofar shiga Masallacin, to zaka koma gida da qafarka haka kuwa don za’a sace maka shi. Haka nan kullum zaka ji labarin an sace Motar wane a Masallaci, an sace Mashin din wane, to wanda ya sace abu a masallaci ka fada min abunda ba zai aikata ba na laifi?

Babu wa’azin da yakai mutuwa, domin idan kaje maqabarta gawarwaki ne kwakkwance, tsofaffin kushewa, da sababbi, yara da manya, maza da mata, amma Talakan Nigeria har a maqabarta bai daina yin sata ba!
Mau ginin kabari ya baiwa mutum Amanar riqon wayar Salula, ya hana, ya riqe wayar ayi cikiyar duniya ba zaka ji wanda yace ga wayar ba. A Wasu gurare har kayan aikin tonon Qabarin ake sacewa Diga ko Chebir.

Kaje Qauye kayi karambani kace zaka gwada yin Noma. Idan ka dora wani Talaka dan uwa akan harkar noman naka, zaka ga yadda zai cinye amanar ka. Saboda satar mashin, Talakan Nigeria yana yima mutum yankan rago, saboda ya qwace ma wani mashin kawai, Lebura mai yin gini zai sace Simintin da suke yin gini don ya sami kudi saboda tsabar ha’inci, Kanikawa ma hakan take.

Malaman makarantun kwana idan an kawo musu abincin ɗalibai daga gomnati su sace abincin su sayar da wani su kai wani gidajensu, su dinga ci da iyalansu, Idan magani aka kawo domin ɗalibai su sace su sayar,

Ka bude shago ka dauko wani talaka bayan ka zuba hajah, ka dora shi a kan dukiyar ka kaga yadda zai ci amanar ka.

Ayanzu damuke Cikin Watan Azumin Ramadana Kaduba yadda ‘Yan kasuwa Musulmai suke tasarifi da kayayyakin masarufi komai ya tsawwale tsada fau saboda Musulmai su shaa wahala dan kawai su sami kudi.

Amma a haka muna son shugabanci ne irin Shugabancin Qasar Saudiyya

Yadda mu Talakawan Nigeria halin mu da ɗabi’un mu suke, Irin halaye da ɗabi’un Talakawan Qasar Saudiyya kenan?

Duk yawan mu bamu kai ‘yan China yawa ba, amma suna jin dadin rayuwa, domin yadda Talakawansu suke, haka shugabannin su suke, Allah baya zalunci!!!

Duk me son ya girbe Dawa, to ya shuka dawa Ba yadda za’ayi mu talakawan Nigeria mu kasance:
Barayi, Maha’inta
Marasa tausayi,
Marasa kishin qasa, sannan kuma Allah ya bamu shugabanni ba barayi ba, ba maha’inta ba, masu kishin qasa, marasa mugunta!!!

In banda Allah mai tausayin bayinsa ne, hakika, Allah Yaa tausaya mana ma, tunda Ya bamu shugabanni irin wa’yannan, wadanda idan zalincin su yafi haka, bai kamata muce komai ba saboda yadda suke haka muma muke, wani lokaci gara halin shigabannin ma bisa ga halin mu. Ba lokacin da mu talakawa muke tuhumar kanmu, kullum tuhumarmu kan shugabannin mu take tsayawa, bayan mune silar samuwan Azzaluman Shugabannin saboda zalincin mu!
Idan Talakan Nigeria ya sami wata dama, zalincin da zaiyi, Wallahi wasu shugabannin ma ba zasu yi ba!

Bamu da aiki sai yawan qorafi kan shugabanni kuma munqi mu gyara namu matsalolin. Matsalolin shugabannin mu muke leqe muke hange, wanda hakan yasa muke zaune cikin qasqanci da wulaqanci.

Matuqar bamu sauya daga yadda muke ba, haka shima Allah ba zai sauya mana ba. Idan da wanda ya san wata qasa a duniya wacce talakawa suke aikata irin abinda mu Talakawan Nigeria muke Aikatawa kuma Allah yabasu Shugabanni masu kirki ya fada mana wannan qasar a duniya muji, wacce qasa ce???

Dan uwa zan baka Assignment ka zauna kai kadai kayi tadabburin duk wata qasa a cikin wannan duniyar Wallahi za kaga yadda Talakawan Qasar suke haka Shugabannin su suke Allah baya zalinci, Duk gonar da aka shuka shinkafa to shinkafar za’a cire, Yadda ba wanda ya taba noma Doya ya tono Dankali, haka zalika ba yadda za’ayi Talakawan Nigeria a irin miyagun ɗabi’un mu Allah ya bamu shugabanni ba masu mayagun ɗabi’u ba!!!
Mu Talakawan Nigeria mun maida Al-amarin gyaruwar Nigeria ne kan Shugabannin mu su kadai mu banda mu, a haka muke son qasar ta gyaru ba tare da gudunmuwar mu ba.

Shi yasa qasar take yadda take jiya, yau Wa’yanda suke Mulkarmu a yau idan muka duba ba wasu sababbi bane, wa’yanda suka mulki iyaye da kakannin mu sune yau suke mulkarmu har yanxu ba sauyawa akayi ba, Gobe da jibi sune zasu mulki ‘ya’yanmu da jikokinmu idan sun mutu ‘ya’yansu ne zasu ci gaba da mulkar mu!

Talakawan Nigeria, Qalu Balen mu!
Wallahi idan bamu gyara ba haka qasar zata ci gaba da tafiyar Hawainiya Jiya tafi yau Yau tafi Gobe.

Duk me son ya girbe Dawa, to dole ya shuka dawa.

Aminu Bala Madobi ya rubuta daga Kano

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here