Zaɓen 2023: APC za ta fara sayar da fom ɗin takara a yau

APC 2 1
APC 2 1

A yau Talata ne jam’iyyar APC, za ta fara sayar da fom ɗin na gani ina so ga masu sha’awar tsayawa takarar muƙamai daban-daban gabanin zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Ya kamata a fara sayar da fom ɗin a ranar Asabar ɗin da ta gabata, amma an ɗage har zuwa yau sakamakon gazawar da ɗan kwangila ya yi wajen kai fam ɗin.

A kan haka ne, kwamitin ayyuka na jam’iyyar NWC ya umurci sakatarorin jihohi 36 da su karɓi fom ɗin daga hannun ƴan takarar da ke neman kujerar majalisun dokokin jiha.

Hakan dai na daga cikin ƙoƙarin da jam’iyya mai mulki ta yi na ganin ta cika jadawalin ayyuka da kuma jadawalin hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC.

Sakatariyar ta kasa ce za ta siyar da fom ɗin ga masu neman takarar kujerar majalisar wakilai ta kasa da na takarar kujerar shugaban kasa a wurare uku da aka keɓe.

Kwamitin ayyuka na jam’iyyar ta APC, ya kuma ba da umarnin a sayar da fom ɗin tsayawa takarar majalisar dokokin jihar a shalkwatar ta ta jihohi.

Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa Mista Felix Morka ya tabbatar wa manema labarai jiya Litinin cewa za a fara sayar da fom a yau.

A cewar sa, “A gobe Talata ne za mu fara siyarwa. Ba da daɗewa ba za a fitar da ƙa’idodin yadda tsarin ayyukan mu zai gudana a kafofin mu na sada zumanta, Yayin da za a sayar da fom ɗin majalisun dokokin jiha a matakin jiha a faɗin kasa, sauran kuma za a sayar da su a nan Sakatariyar kasa.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here