A ranar Laraba ne shugaban kasa, Bola Tinubu ya gana da tsaffin gwamnonin jihar Rivers, Nyesom Wike, da na jihar Kaduna, Malam Nasir el-Rufai, a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Idan dai za a iya tunawa, tsaffin gwamnonin biyu, wadanda za a nada a matsayin ministoci, duk da cewa majalisar dattawa ta gama tantance Wike yayin da take-sama-tana-dabo kan El-Rufai.
Tsoffin gwamnonin sun isa gidan gwamnatin alokuta daban daban.
Wike ya isa fadar da misalin karfe 1:40 na rana, yayin da El-Rufai ya shiga bangaren shugaban kasa na Aso Rock da karfe 2 na rana.
Majiyoyi a fadar shugaban kasa ta bayyana cewa ana kokarin ganin majalisar dattawa ta tabbatar da sunan Mallam El-Rufai domin nada shi minista.













































