Jami’yyar LP ta dakatar ‘yar Majalisa kan kalamanta da ya shafi kisan gilla da Isra’ila ke yi. ‘Yar Majalisar, Osamor Kate wacce asali ‘yar Najeriya ce ta bayyana ra’ayinta ne kan kisan da Isra’ila ke aikatawa kan Gaza.
Kate ta kwatanta kisan gillar da Isra’ila ke yi kan Gaza da wanda aka yi kan Yahudawa.
Tuni Kate da ke wakiltar Edmonton ta ba da hakuri kan kalamanta da ta yi a ranar Lahadi 28 ga watan Janairu.
Har ila yau, Yahudawa sun yi Allah wadai da kalaman Kate wanda ta yi misali da su. Mai ladabtarwa a Majalisar ya dakatar da ita tare da kaddamar da bincike kan lamarin don daukar mataki.
Daily Trust ta tattaro cewa Kate ta bayyana haka ne yayin bikin tunawa da kisan Yahudawa da sauran wadanda aka ci zarafi a duniya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa ana bikin Holocaust Memorial Day (HMD) don nuna alhini kan kisan Yahudawa miliyan shida a duniya.
Kate ta rubuta a shafinta na X kamar haka: “Gobe ne ranar tunawa da kisan Yahudawa miliyan shida a duniya da sauran mutane karkashin jagorancin Nazi. “Sai kuma kisan gillar baya-bayan nan da aka yi a Cambodia da Rwanda da Bosnia da kuma abin da ya faru yanzu a Gaza.”