
Dakta Abdullahi Ganduje, ya yi murabus daga mukaminsa na shugaban jam’iyyar APC na kasa.
Ganduje, wanda ya yi gwamnan Kano daga shekarar 2015 zuwa 2023, ya sanar da murabus ɗinsa ne nan take.
Ya zuwa yanzu ba a san hakikanin abin da ya sanya murabus din nasa ba, sai dai wani babban jigo a jam’iyyar ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce, “Eh gaskiya ne, ya yi murabus.”
Majiyoyi sun bayyana cewa tun da farko an kwashe kayan Ganduje daga ofishinsa dake sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa, lamarin da ya kara rura wutar cece-kuce.
Wannan lamari dai, ya jefa shalkwatar jam’iyyar cikin rudani, inda ma’aikata da maziyarta suka kadu da wannan labari na bazata.












































