Ƙungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Manyan Ma’aikata a Najeriya (PENGASSAN) ta bayar da umarni ga mambobinta da su dakatar da kai iskar gas zuwa Kamfanin Mai na Dangote da gaggawa.
A wata wasiƙa da Sakatare Janar na ƙungiyar, Comrade Lumumba Okugbawa ya sanya wa hannu a ranar Juma’a, PENGASSAN ta zargi shugabancin kamfanin da korar ma’aikatan da ke da rajin shiga ƙungiya, tare da yada bayanan ƙarya maimakon tattaunawa da gaskiya.
Ƙungiyar ta umurci dukkan shugabannin rassanta musamman na kamfanin NGIC da su tabbatar da dakatar da kai gas zuwa kamfanin ba tare da ɓata lokaci ba.
Haka kuma umarnin ya haɗa da rufe dukkan bututun iskar gas da mai zuwa masana’antar da kuma dakatar da lodin kaya ga jiragen ruwa da ke kan hanyarsu zuwa wurin.
Karin labari: Malala ta ziyarci Najeriya domin ƙarfafa ilimin ƴaƴa mata
Hakanan, PENGASSAN ta ba da umarni ga rassanta a manyan kamfanonin man fetur da iskar gas irin su TotalEnergies, Chevron, Seplat, Shell Nigeria Gas, Oando da kamfanin gas na Nigerian Gas Infrastructure Company da su dakatar da kai duka mai da iskar gas zuwa kamfanin.
Ƙungiyar ta bayyana wannan mataki a matsayin kariya ga haƙƙin ma’aikata na tsarin kundin tsarin mulki da ke basu damar shiga ƙungiya.
Duk da haka, rukunin Dangote a baya ya musanta zargin cewa an kori ma’aikata da yawa, inda ta ce ƙalilan aka shafa ne a wani yunƙurin kare masana’antar daga lalata.
Kamfanin ya ƙara da cewa sama da ma’aikata 3,000 na Najeriya har yanzu suna aiki a masana’antar, tare da tabbatar da cewa kowanne ma’aikaci na da ‘yancin yanke shawarar shiga ƙungiya ko akasin haka.













































