Jam’iyyar PDP ta dage wa’adin mika takardun tsayawa takara har sai abinda hali yayi

Debo Ologunagba PDP spokesperson 750x430

Kwamitin shirya babban taron kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya sanar da dage wa’adin mika fom ɗin nuna sha’awa da na tsayawa takara na ‘yan takara har sai abinda hali ya yi.

Jam’iyyar ta fitar da sanarwa a Abuja ta bakin sakataren kwamitin yada labarai, Mista Debo Ologunagba, inda ta bayyana cewa an dage wa’adin daga ranar Juma’a 26 ga Satumba da aka tsara a baya.

Ologunagba ya ce har yanzu kwamitin bai saka sabon kwanan wata ba, amma da zarar an yanke shawara za a sanar da jama’a.

Haka kuma ya bayyana cewa an dage ranar tantance ‘yan takara wadda a baya aka tsara a yi a Talata 30 ga Satumba.

Ya ce dagewar ta zama dole ne domin tabbatar da shirye-shiryen gudanar da aikin cikin sauƙi da tsari mai kyau.

Ologunagba ya yi kira ga dukkan masu neman tsayawa takara da su lura da wannan canji su kuma yi biyayya da sabon jadawalin da za a fitar daga baya.

An dai shirya gudanar da babban taron zaben shugabannin jam’iyyar a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba a birnin Ibadan.

NAN

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here