
Hukumar kula da sufurin Jiragen ƙasa ta ƙasa (NRC) ta bayyana cewa sufurin jirgin ƙasa tsakanin Abuja da Kaduna zai fara aiki nan da mako mai zuwa.
Sanarwar ta zo ne bayan an kammala gyare-gyare da binciken tsaro a ɓangaren layin jirgin da ya lalace a Asham.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Asabar ta bakin babban jami’in hulɗa da jama’a na NRC, Mista Callistus Unyimadu.
Sai dai hukumar ta ce za a bayyana cikakkun bayanai kan ranar da za a fara aiki da jadawalin tashi daga baya a cikin kwanaki masu zuwa.
Karin labari: Hukumar NRC ta bayyana lokacin da jirgin kasan Kaduna zuwa Kano zai fara aiki
Hukumar ta bayyana cewa tun bayan faduwar jirgin a ranar 26 ga watan Agusta, 2025, ta yi aiki tukuru wajen dawo da ingancin layin da kuma jiragen bisa ƙa’idojin tsaro na duniya.
A cewar hukumar, a cikin fasinjoji 583 da ke cikin jirgin da ya faɗi, ta riga ta mayar da kuɗin tikitin mutane 512, yayin da ake ci gaba da biyan ragowar domin kowa ya samu hakkinsa.
NRC ta gode wa fasinjoji bisa haƙuri da fahimta, tare da tabbatar musu cewa tsaro, jin daɗi da walwalar su su ne babban abin da take bai wa muhimmanci.
Haka kuma ta yabawa gudunmawar ma’aikatar sufuri ta tarayya, jami’an tsaro, kafafen yaɗa labarai da sauran masu ruwa da tsaki wajen dawo da ayyukan.
Rahotanni sun nuna cewa faduwar jirgin ta auku ne a hanyar Kaduna, jim kaɗan bayan tashin jirgin daga Abuja da misalin ƙarfe 11 na safe.











































