Gwamna Kano zai naɗa kwamishinoni biyu, da Babban Lauya na Jiha

WhatsApp Image 2025 04 25 at 08.51.59 750x430

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya tura sunayen mutane biyu zuwa majalisar dokokin jihar Kano domin tabbatar da su a matsayin kwamishinoni da mambobin majalisar zartarwa ta jiha.

Wannan na ƙunshe ne cikin sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Asabar.

Daga cikin waɗanda aka naɗa shi ne Barrista Abdulkarim Kabir Maude, ɗan asalin Minjibir, wanda ake shirin ba shi lambar girmamawa ta SAN a gaban kotun ƙoli yau Lahadi.

Maude, mai shekaru 40, lauya ne mai basira wanda ya yi karatun digiri a fannin lauya a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.

Ya kasance memba a ƙungiyar lauyoyin Najeriya da kuma ƙungiyar masu sasanta rikice-rikice ta Najeriya.

Barrista Maude ya yi aiki a fannoni daban-daban ciki har da harkokin gudanar da ofis, shari’o’i a kotu, hulɗa da kwastomomi, rubuce-rubucen shari’a, harkokin kamfanoni da kuma gudanar da kadarori.

Ya yi aiki a matsayin shugaban ofishin wani babban kamfani na shari’a a Najeriya, inda ya samu gogewa na fiye da shekara goma.

Ya yi karatun digiri na biyu a fannin dokokin tattalin arziki na ƙasa da ƙasa a Jami’ar Maryam Abacha ta Nijar, da digiri na biyu a dokokin kasuwanci a Jami’ar Bayero Kano, sannan ya samu shaidar BL daga Makarantar Lauyoyi ta Najeriya, Abuja.

Haka kuma, an naɗa Dr. Aliyu Isa Aliyu, Farfesa mai taimako a fannin lissafi, wanda ya tara ƙwarewa a fannoni na ilimi da gudanarwa.

Ya yi karatun digiri na farko a Jami’ar Bayero Kano, ya samu digiri na biyu daga Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jordan, sannan ya yi digirin digirgir a Jami’ar Firat ta ƙasar Turkiyya.

Ya fara koyarwa a Jami’ar Tarayya Dutse a shekarar 2014, inda daga baya ya zama Farfesa mai taimako a Jami’ar Northwest Kano.

Dr. Aliyu ya kara samun ƙwarewa a matsayin mai bincike a Jami’ar Sun Yat-Sen ta ƙasar Sin, da kuma a Jami’ar Near East ta Cyprus.

Tun daga shekarar 2023 yake aiki a matsayin Darakta Janar na hukumar ƙididdiga ta Jihar Kano.

Yana da shekaru 41, kuma yana daga cikin manyan masu bincike a fannin lissafi a duniya, kana yana daga cikin waɗanda suka amfana da tallafin karatun ƙasashen waje na Kwankwasiyya.

Ya yi aiki a matsayin Sakataren Kuɗi na jam’iyyar NNPP a Kano.

A wani ɓangare daban, Gwamna Yusuf ya amince da naɗin Barrista Salisu Muhammad Tahir a matsayin sabon Babban Lauya kuma Babban Sakatare na ma’aikatar shari’a ta jihar.

Kafin wannan naɗi, Barrista Tahir ya riƙe mukamin Daraktan Gurfanarwa da Ƙara a ma’aikatar shari’a ta jiha.

An umarci Shugaban Ma’aikata da ya tabbatar da an kammala dukkan matakan gudanarwa kafin sabon Babban Lauyan ya fara aiki a ranar Litinin, 29 ga Satumba, 2025.

Da yake naɗa waɗannan sababbin matasa cikin majalisar zartarwa, Gwamna Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatinsa na samar da nagarta, ƙwarewa, da gaskiya a cikin hidimar jama’a.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here