Shettima ya tafi Jamus bayan kammala taron MDD karo na 80

Shettima departs new 750x430

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bar birnin New York na ƙasar Amurka bayan ya wakilci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaman Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80.

Shettima yanzu ya nufi ƙasar Jamus, inda zai gana da jami’an bankin Deutsche Bank domin tattaunawa kan hanyoyin haɗin gwiwa da tallafi ga shirye-shiryen ci gaban Najeriya.

A cewar mai magana da yawunsa, Stanley Nkwocha, yayin taron MDD na 80, Shettima ya samu yabo daga Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres, bisa ƙoƙarin Najeriya na neman zama ɗan dindindin a Kwamitin Tsaro na MDD.

Mataimakin shugaban ƙasan ya kuma gabatar da damar da Najeriya ke da ita ta dala biliyan 200 a fannin sauyin makamashi ga masu zuba jari na duniya tare da ƙarfafa dangantaka da Birtaniya kan harkokin kasuwanci, tsaro da batun ƙaura.

Labari mai alaƙa: UNGA80: Shettima ya gana da Guterres,tare da tattauna batun neman kujera a kwamitin tsarona MDD

A cikin jawabin da ya mika a madadin shugaban ƙasa, Shettima ya jaddada bukatar yin garambawul a Majalisar Ɗinkin Duniya, tare da neman Najeriya ta samu kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro.

Ya kuma bukaci nahiyar Afrika ta riƙe iko da dukiyar ma’adinaita da kimarsu ta kai dala biliyan 700, da kuma ƙara zuba jari a shirin saka al’umma cikin duniyar fasahar zamani.

Haka kuma, Shettima ya gana da Asusun Gates domin tattaunawa kan faɗaɗa harkokin kiwon lafiya da ilimi a Najeriya, tare da ƙarfafa matsayin ƙasar a matsayin cibiyar kasuwancin Afrrka da darajarta ta kai dala tiriliyan 3.4.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here