Gwamnatin tarayya a ranar Lahadi ta karyata zarge-zargen da wasu kafafen yada labarai na waje da masu sharhi a internet suka yi cewa ‘yan ta’adda a Najeriya na gudanar da kisan kiyashi na musamman ga Kiristoci.
Ministan yaɗa labarai da tsare-tsaren ƙasa, Muhammad Idris, a cikin wata sanarwa ya bayyana waɗannan zarge-zarge a matsayin karya, masu haddasa rabuwar kawuna a ƙasar.
Ya ce ya kamata a gane cewa matsalolin tsaro a Najeriya ba na addini ba ne.
A cewarsa, ɗaukar matsalolin tsaro na ƙasar a matsayin wani shiri na kai hari ga wata ƙungiyar addini ɗaya babban kuskure ne.
Ya ce duk da cewa akwai kalubale na ta’addanci da aikata miyagun laifuka, hakan bai taɓa kasancewa da niyyar kai wa Kiristoci hari ba.
Idris ya jaddada cewa ‘yan ta’adda sun kai hare-hare kan ‘yan Najeriya daga addinai daban-daban, ciki har da Musulmai da Kiristoci, da ma waɗanda ba su da wata alaƙa da addini.
Ya ce waɗannan miyagu suna kai hari ne ga duk wanda bai amince da akidar kashe-kashen su ba.
Ministan ya bayyana cewa tsakanin watan Mayu 2023 zuwa Fabrairu 2025, jami’an tsaro sun kashe ‘yan ta’adda da sauran miyagu sama da 13,500 tare da ceto wadanda kusan 10,000 a fadin ƙasar.
Haka kuma an kama manyan shugabannin ƙungiyar Ansaru a wani shirin yaki da ta’addanci da aka gudanar.
Karanta: Shettima ya tafi Jamus bayan kammala taron MDD karo na 80
Ya ƙara da cewa, zuwa yanzu an yi shari’a kan gungun masu ta’addanci bakwai, inda aka yi hukunci ga sama da 700 kan masu hannu da ake zargi da Boko Haram.
Ya kuma bayyana cewa addinin Kiristanci ba a take shi a Najeriya, tare da tunatar da cewa a yanzu shugabannin rundunar soji da na ‘yan sanda Kiristoci ne, abin da ke nuna daidaito a shugabancin ƙasa.
Idris ya kuma tunatar da cewa a watan Maris na wannan shekara, an bai wa malamin Kirista, Fasto James Movel Wuye, da limamin Musulmi, Dr. Muhammad Nurayn Ashafa, lambar yabo ta zaman lafiya ta Commonwealth saboda ƙoƙarinsu na haɗa kan al’umma.
Ya roƙi kafafen yada labarai na waje da masu sharhi da su guji yada maganganun rarrabuwar kai, su maida hankali wajen tallafa wa ƙoƙarin Najeriya na yaƙi da ta’addanci da sauran laifuka.













































