Gwamnatin tarayya ta bayar da tabbacin cewa za a kammala aikin babbar hanyar Legas zuwa Abuja cikin shekaru 4.
Ministan ayyuka, David Umahi ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai ranar Asabar, a Abuja.
Umahi ya lura cewa tuki daga Legas zuwa Abuja zai dauki sa’o’i 4 akan babbar hanyar idan an kammala ta.
Ya ce za a yi hanyar ne da siminti kawai, inda ya ce ya fi kwalta arha.