Gwamnatin tarayya ta shiga tsakani a rikicin masana’antu da ke tsakanin ƙungiyar ma’aikatan manyan jami’an mai da iskar gas ta Najeriya (PENGASSAN) da kuma kamfanin sarrafa mai na Dangote, bayan sanarwar ƙungiyar na fara yajin aiki a fadin ƙasar nan.
A wata sanarwa da shugaban sashen bayanai da hulɗa da jama’a na ma’aikatar ƙwadago, Patience Onuobia, ta fitar a ranar Lahadi, ministan ƙwadago da ayyukan yi, Muhammad Maigari Dingyadi, ya roƙi PENGASSAN da ta dakatar da yajin aikin da ta tsara farawa a ranar Litinin, 29 ga Satumba, 2025.
Dingyadi ya bayyana cewa ma’aikatarsa ta gayyaci shugabannin PENGASSAN tare da hukumar gudanarwar kamfanin mai na Dangote zuwa wani zaman gaggawa na sasanci a ofishinsa a ranar Litinin.
Ya jaddada cewa tattaunawar ita ce hanya mafi dacewa wajen kaucewa tsananta rikicin.
Labari mai alaƙa: Matatar Man Ɗangote: PENGASSAN sun fara yajin aiki a faɗin ƙasa sakamakon korar ma’aikata da kamfanin ya yi
Ya yi gargadi kan cewa duk wani yajin aiki a fannin mai da iskar gas zai iya haifar da mummunan tasiri ga tattalin arzikin ƙasa da kuma zaman lafiyarta.
A cewarsa, wannan fanni shi ne ginshiƙin tattalin arzikin Najeriya, kuma duk wani tsaiko zai haifar da asarar kuɗaɗe masu yawa da ƙarin wahalhalu ga al’umma.
Dingyadi ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da yin duk mai yiwuwa domin warware rikicin cikin amfanin ƙasa da kuma tabbatar da adalci ga ɓangarorin biyu. Ya yi kira ga PENGASSAN da ta janye yajin aikin da ta sanar.












































