Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta yi karin bayani kan yadda masu safarqr kwayoyi suka tuntubi tawagar DCP Abba Kyari, wanda aka dakatar saboda wasu zarge-zarge.
Bayanin ya fito ne a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar a ranar Laraba, kwanaki bayan bayyanar labarin cinikin hodar iblis mai nauyin kilogiram 25 da Kyari ya yi.
“Domin gyara wasu kura-kurai da aka samu a cikin bayanan da jama’a ke yadawa cewa jami’an NDLEA a filin jirgin sama na Enugu su ne suka samu bayanai daga ma’aikatan jirgin kan masu safarar kwayoyi da suka fito daga Addis Ababa, hukumar na so ta bayyana tattaunawar da Abba Kyari ya yi da Jami’in mu na boye da kuma wani bangare na bayanin ASP James Bawa kamar yadda aka bayyana a rahoton ‘yan sanda wanda aka mika kwafinsa ga hukumar.
“Za ku iya tuna cewa bayan NDLEA ta nemi Kyari da sauran wadanda ake zargi domin su yi musu tambayoyi, ‘yan sanda sun tsare su tare da yi musu nasu tambayoyin, inda daga bisa suka mika su ga NDLEA tare da rahoton tambayoyin da aka yi musu.” in ji sanarwar.
“A cewar rahoton binciken ‘yan sanda, ASP James Bawa a cikin sanarwar da ya yi wa ‘yan sanda ya bayyana cewa ‘wani mai ba da labari mai suna IK dan kasar Brazil ne ya kira shi ya shaida masa cewa wani mai dauke da muggan kwayoyi zai iso cikin jirgin Ethiopian Airlines a Enugu.
Ya kara da cewa wani mai nuni daga IK, dan kasar Brazil ya gana da shi da misalin karfe 1420 a ranar 19 ga Janairu, 2022 a wajen filin jirgin sama kuma ya nuna masa hoton dan aike. Daga baya, sun hangi wanda ake zargin yayin da ya fito daga tashar jirgin sama bayan duk ka’idojin isowa, kuma an kama shi tare da wani abokinsa.”
Ya kara da cewa: “A cikin nasa tattaunawar da ya yi da jami’in mu na boye, Abba Kyari ya ce: ‘su Masu kwadayi ne (yana nufin masu ba da bayanai na NDLEA), mun yi kokarin karbar kashi 40% amma suka ki, sai kashi 50%. , sun san ginshiƙin yarjejeniyar da kyau, su ne suke yin kayan.
“Daga Brazil, daya daga cikin masu ba da labari ya raka shi zuwa Habasha. Kun fahimta; daya daga cikin masu ba da labarin ya raka kayan zuwa Habasha, daya daga cikin masu ba mu bayanai. Shi ne yaron babban baron.
A cewar sanarwar, Mista Babafemi ya tabbatar da cewa labarin bai bar kokwanto ba kuma ya tabbatar da wanda kungiyar ke da alaka da su da kuma tsarin aikinsu.
Sanarwar ta ba da tabbacin cewa hukumar ba za ta bijire wa binciken da aka yi kan shaida ba wanda ba zai hana duk wanda aka samu da hannu a ciki ba.












































