Gwamnatin Kano ta biya Naira Biliyan 21 daga cikin Naira Biliyan 48.6 na kudaden fansho da gwamnatocin Kwankwaso da Ganduje suka gadar mata

imgonline com ua twotoone Ge8Fz15MRK 750x430

Ya zuwa yanzu gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta biya sama da Naira biliyan 21 na kudaden fansho daga cikin basussukan Naira biliyan 48.6 da ta gada daga gwamnatocin Sanata Rabi’u Kwankwaso da Dr. Abdullahi Ganduje a jihar.

Shugaban amintattu na asusun fansho na jihar Kano, Alhaji Habu Fagge ne ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano.

“Halin da hukumar ta kasance a lokacin da gwamnati mai ci ta karbi ragamar mulki abu ne mai matukar tayar da hankali.

“’Yan fansho sun sha wahala ba bisa ka’ida ba a gwamnatin da ta shude, inda a wasu lokutan sukan rasa rabin abin da suke da shi a kowane wata.

Karanta: Shugaba Tinubu ya daga likafar fanshon jami’an sojin ruwa

“A wani lokaci, ‘yan fansho da ke karbar Naira 6,000 an cire musu Naira 3,000 ba tare da wani bayani ba, ba mu iya samun wata tabbatacciyar hanyar cire kudaden ba,” inji shi.

A cewar shugaban zartaswar gwamnatin da ta gabata ta ci bashin ne daga asusun fansho.

Ya ce wani bangare na warware bashin ya fara ne a lokacin da Gwamna Abba Yusuf ya amince da a rika cirewa daga majiyar kudaden fansho, da maido da kudaden da ake biyan su a kai a kai da kuma baiwa hukumar damar samun kashi 100 cikin 100 na kudaden fansho duk wata.

“Mun gaji Naira Biliyan 48.6 a matsayin alawus-alawus sannan kuma sai da muka fitar da Naira biliyan 75 da aka karba a kananan hukumomi da wasu Ma’aikatu.

“Duk da haka, mun yi nasarar kashe Naira biliyan 16 ya zuwa yanzu, tare da wasu Naira biliyan 5 da aka shirya za a biya nan ba da jimawa ba,” in ji Fagge.

Ya yaba wa gwamnan kan yadda ya nuna tausayawa, inda ya ce “duk da cewa an gaji bashin, gwamnan ya dauki nauyi tare da tabbatar da an biya, saboda kawai ya damu da ‘yan fansho.

Shugaban ya kuma yi karin haske kan yadda hukumar ke tafiyar da ayyukan gidajen biranen Bandirawo, Kwankwasiyya da Amana a jihar.

A karkashin gwamnatin da ta shude, ya ce, hukumar ta bayar da rancen kudi don zuba jarin kadarorin, wanda ya haifar da cece-kuce a cikin shari’a, kuma bayan hukuncin da kotu ta yanke da tattaunawa, an ware gidaje 324 ga hukumar fansho a matsayin sulhu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here