Dalilin da ya sa gwamnatin tarayya ta dawo da darasin tarihi cikin kundin tsarin karatu – Minista

Alausa education minister

Gwamnatin tarayya ta ce ta dawo da darasin tarihin Najeriya a matsayin darasi na dole a cikin kundin tsarin karatu a mataki na farko domin inganta ɗan asalin ƙasa, haɗin kai, kishin ƙasa da kuma ɗa’a a tsakanin matasan Najeriya.

Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Mrs Folasade Boriowo, ta fitar a Abuja ranar Laraba.

A cikin sanarwar, ministan ya ce an tsara sabon kundin karatun ne domin farfaɗo da alfahari da tarihin ƙasar, gina wayewar ɗan ƙasa, tare da ba matasa ilimi da ƙimomin da za su taimaka wajen gina ƙasa mai ɗorewa.

Ya kuma yi godiya ga Shugaba Bola Tinubu saboda goyon bayan wannan sauyi karkashin shirin Sabon Fatan Najeriya.

Alausa ya jaddada cewa tarihi ba wai kawai rubuce-rubucen abin da ya gabata ba ne, illa kuwa tushen da zai taimaka wajen gina ’yan ƙasa masu kishin ƙasa da ɗabi’a.

Ya ce wannan shi ne karo na farko cikin shekaru masu yawa da ɗaliban firamare daga aji ɗaya zuwa uku za su fara koyon tarihin Najeriya ba tare da yankewa ba.

Ya bayyana cewa daga aji na ɗaya zuwa na shida, dalibai za su koyi asalin Najeriya, jarumai da jarumawa, sarakuna da tsarin gargajiya, gadon al’adu, ci gaban siyasa, yanayin ƙasa, tattalin arziƙi, addinai, mulkin mallaka da kuma tafiyar mulkin ƙasar bayan samun ’yancin kai.

Haka kuma, daliban JSS1 zuwa JSS3 za su koyi darasin Ilmin Ɗan ƙasa da Tarihi, wanda ya haɗa darussan tarihin tsoffin shugabannin Najeriya, daular gargajiya, ƙasashen Yammacin Afirka, kasuwancin sahara, hulɗa da Turawa, haɗaɗɗiyar Najeriya, yaƙin neman ’yanci, da tafiyar dimokuraɗiyya, tare da darussan kishin ƙasa domin ƙarfafa ɗan asalin ƙasa da haɗin kai.

A cewar ministan, wannan sauyi babban kyauta ne ga ƙasa, domin yana haɗa yara da tushensu tare da inganta alfahari, haɗin kai da jajircewa wajen ci gaban Najeriya.

Karanta: Jihar Jigawa ta amince da kashe Naira biliyan 15 a fannin samar da ilimi a matakin farko

Ya ƙara da cewa haɗa darasin ɗabi’a da ilimin ƙasa cikin sabon tsarin karatu zai taimaka wajen koya wa ɗalibai girmama bambance-bambance, mutunta hukumomi da bayar da gudummawa ga cigaban al’umma.

Ya bayyana cewa ma’aikatar ta riga ta fitar da kundin Tarihin Najeriya da aka sabunta domin aji na 1 zuwa 6 da kuma JSS1 zuwa 3.

Don tabbatar da nasarar aiwatarwa, ya ce za su yi aiki tare da masu ruwa da tsaki wajen samar da kayan aiki, sake horas da malamai da kuma inganta tsarin sa ido da tantancewa.

Dakta Alausa ya yi kira ga iyaye, malamai da al’umma gaba ɗaya da su rungumi wannan sauyi a matsayin nauyi tare wajen tarbiyyar yan ƙasa masu ladabi masu kishin kasa da hangen nesa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here