Kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles ta sauka daga matakin da take na 45 a Duniya a jadawalin da hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA ke fitarwa duk wata na kasashen da sukafi kokari.
Hukumar ta FIFA ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a shafinta na internet a ranar Alhamis.
Haka zalika kungiyar ta Super Eagles dake nan Najeriya da mai horar da yan wasanta Eric Chelle ke jagoranta ta fita daga jerin kungiyoyi biyar dake kan gaba a Afrika.
Najeriya da ta lashe kyautar Azurfa a gasar kasashen Afrika ta AFCON da akai a shekarar 2024, sau biyu tana sauka daga matakin da take a Jere sakamakon rashin kokari da ta yi wasannin baya bayan nan data buga.
Yanzu haka dai kasar Morocco ce a matsayin ta 11 a Duniya, inda take a matsayin ta 1 a Afrika Sai Senegal ta biyu da Egypt ta Uku yayin da Algeria ke a matsayin ta 5 sai Najeriya da take a matsayin ta 6.
Kasar Spain ce ta kasance a matsayin ta 1 a Duniya bayan data sauke kasar Argentina da take a matsayin ta daya a baya.
kasar France ce dai ta kasance a matsayin ta 2 a Duniya.
Haka zalika kungiyar kwallon kafar kasar Spain ce dai a matsayin ta 1 a Duniya bayan data maye gurbin kasar Amurka, yayin kungiyar kwallon kafar Mata ta Najeriya Super Falcon taci gaba da zama a matakin da take na 36 a Duniya.













































