Gwamnatin tarayya ta ce ta rarraba Naira biliyan 330 a matsayin tallafin kuɗi ga talakawa da marasa galihu ta ofishin ƙasa na daidaita tsare-tsaren kariya ta zamantakewa (NASSCO).
Ministan kuɗi kuma babban mai kula da tattalin arziƙin ƙasa, Wale Edun, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a Abuja, yayin taron kwamiti na musamman na shugaban ƙasa kan shirin saka hannun jari na zamantakewa.
Ya ce wannan mataki na daga cikin shirye-shiryen shugaban ƙasa Bola Tinubu don rage wa al’umma raɗaɗin tsadar rayuwa da aka samu sakamakon sauye-sauyen da gwamnati ta ɗauka.
Edun ya ce shirin tallafin ya koma turba, inda aka tanadar da shi domin taimaka wa jama’a su jure da hauhawar farashin kayayyaki.
Ya bayyana cewa an ƙunshe kusan gidaje miliyan 19.7 masu fama da ƙuncin rayuwa a cikin rajistar ƙasa, wanda ya haura mutane miliyan 70 baki ɗaya.
A cewarsa, tallafin kuɗin, wanda aka samo daga ɗaukar bashin dala miliyan 800 daga babban bankin duniya, ya kai ga gidaje miliyan 15.
Karin labari: FAAC: Gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi sun raba Naira Tiriliyan 2.2 na Agusta
Daga cikinsu, gidaje miliyan 8.5 sun riga sun karɓi aƙalla rabo ɗaya na Naira 25,000, yayin da wasu suka samu biyan sau biyu ko uku.
Ya ce saura gidaje miliyan 7 za a biya su kafin ƙarshen shekara.
Ministan ya ƙara da cewa tsarin na tafiya bisa ingantacciyar hanya, inda ake tantance masu cin gajiyar ta hanyar lambar tantancewa ta ƙasa (NIN), sannan kuma ana biyan kuɗaɗen ne kai tsaye ta asusun banki ko walat ɗin waya.
Ya bayyana cewa daga yanzu za a haɗa shirin a cikin kasafin kuɗin gwamnati na kowace shekara domin tabbatar da dorewarsa.
Shugabar NASSCO na ƙasa, Funmi Olotu, ta ce jinkirin biyan kuɗaɗen ya samo asali ne daga ƙudirin shugaban ƙasa na tabbatar da biyan tallafin ta hanyar NIN domin tabbatar da gaskiya da adalci.
Ta bayyana cewa tsohuwar gwamnati ta shirya biyan Naira 5,000 a kowane wata na tsawon watanni shida, amma gwamnatin yanzu ta sake tsara shirin domin a rika biyan Naira 25,000 a kowane wata na tsawon watanni uku.
Olotu ta ce rajistar ƙasa ta marasa galihu an samar da ita tare da haɗin gwiwar babban bankin duniya, inda aka gina ta bisa kan bayanan zamantakewa fiye da 40, ba tare da wani tasirin siyasa ba.
NAN













































