Rundunar ‘yan sanda a Legas ta tabbatar da cewa wani mai tallata waka, Balogun Eletu, wanda aka fi sani da ‘Sam Larry’ yana tsare a hannun su kuma a halin yanzu yana taimakawa wajen gudanar da bincike kan lamarin mutuwar mawakin nan mai suna Ilerioluwa Aloba, mai shekaru 27, wanda aka fi sani da Mohbad.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Benjamin Hundeyin, ne ya bayyana haka a shafin sa na Twitter da aka tabbatar da @BenHundeyin.