Kotun sauraron kararrakin zaben Gwamnan da ke zamanta a Kaduna ta ce zaben Gwamnan Jihar na shekara ta 2023 bai kammala ba.
Kotun dai a yayin zamanta na ranar Alhamis, ta kuma umarci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ta gudanar da zaben cike gurbi a cikin kwanaki 90 masu zuwa.
Alkalan kotun uku, da ke karkashin jagorancin Mai Shari’a Victor Oviawe, sun ce za a sake zaben ne a rumfuna 24 da ke mazabu bakwai a Kananan Hukumomi hudu mai dauke da kuri’u 16,300.
Muna tafe da karin bayani…