Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar hutu don bikin cikar Najeriya shekaru 63 da samun yancin kai.
Olubunmi Tunji-Ojo, a wata sanarwa da ministan harkokin cikin gida ya fitar a ranar Alhamis, 28 ga watan Satumba a madadin gwamnatin tarayya, ya ayyana Litinin, 2 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu.
A cikin sanarwar tasa, ministan ya taya ‘yan Najeriya na gida da waje murnar samun ‘yancin kai.
A cikin sanarwar da ke dauke da sa hannun sakataren ma’aikatar harkokin cikin gida, Oluwatoyin Akinlade, ministan ya bayyana jajaircewar gwamnatin tarayya na tunkarar kalubalen da ke addabar kasar.