Yanzu-yanzu: Yan Sanda sun kama Muhyi Magaji Rimingado

Muhuyi Magaji Rimingado
Muhuyi Magaji Rimingado

Rundunar ‘Yan sanda dauke da makamai sun kama Tsohon shugaban Hukumar karbar Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, PCACC, Muhuyi Magaji Rimingado.

An kama Muhyi ne a masaukin gwamnan Sokoto da ke Abuja, lokacin da ya je a tantance shi a matsayin dan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar PDP.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan sandan sun tafi da shi nan take bayan an kammala tantance shi inda suka kai shi Shedikwatar Yan sanda dake birnin tarayya Abuja.

Majiyoyin tsaro sun ce nan gaba za a maida shi Kano domin fuskantar tuhuma.

A ranar 28 ga watan Maris, ne ‘yan sandan Kano suja kewaye gidan Muhyi Magaji amma basu kama shi ba.

Idan dai za a iya tunawa, ‘yan sandan sun ajiye motocinsu a kusa da gidansa da ke titin Yahaya Gusau, inda suka yi masa kwanton bauna da misalin karfe 7 na dare.

Gwamnatin Kano ta dakatar da Rimingado ne a watan Yulin shekarar da ta gabata ta 2021 bayan fara bincike kan badakalar kudi da karin kwangiloli da ake zargin an baiwa wasu kamfanoni masu alaka da Gwamnan Kano.

A ranar 1 ga watqn Maris, wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta yi watsi da karar da Muhyi ya shigar gabanta na neman a dakatar da kwamitin bincike da majalisar dokokin jihar Kano ta kafa tare da hana ‘yan sanda gudanar da bincike a kansa da kuma kama shi ko kuma tsoratar da shi, har sai an ci gaba da sauraren karar.

Idan dai za a iya tunawa majalisar dokokin jihar Kano ta gayyaci Muhyi Rimingado kan ya gurfana gaban kwamitinta na wucin gadi da ke binciken karar da aka shigar a kansa ranar 14 ga Yulin shekarar 2021, sai dai Rimingado, ya bada dalilan kiwon lafiya inda ya bukaci karin lokaci don samun lafiya.

A ranar 19 ga watan Yulin 2021, wani babban Asibiti ya aikewa da majalisar dokokin jihar Kano, sakon cewa bayanan lafiyar da Muhyi ya gabatar wa majalisar na bogi ne.

A cikin amsarta mai kwanan watan 19 ga watan Yulin 2021 mai lamba NHA/CMAC/GC/0117/2021/V.I/01, dauke da sanya hsnnun Daraktan Ayyuka na babban Asibitin na Kasa, Dakta A.A. Umar, ya ce an bincika takardun kuma ta gano cewa jabun ne.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here