Rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina ta tabbatar da cewa mutum uku sun mutu yayin da wasu 11 suka jikkata bayan harin da ‘yan bindiga suka kai garin Jikamashi da ke karamar hukumar Musawa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, mataimakin sufeton ‘yan sanda Aliyu Abubakar, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Laraba a Katsina.
Ya bayyana cewa a ranar 10 ga watan Maris da misalin karfe 6:05 na yamma, rundunar ‘yan sanda ta karbi kiran gaggawa daga sashen Musawa cewa wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne dauke da makamai masu hadari sun kai hari kauyen Jikamashi da ke karamar hukumar Musawa.
Ya ce ‘yan bindigar sun jikkata mutane 14 kafin zuwan jami’an tsaro wurin da lamarin ya faru.
Ya kara da cewa bayan samun rahoton, hadin gwiwar jami’an tsaro karkashin jagorancin shugaban sashen ‘yan sanda na Musawa sun gaggauta zuwa wurin da abin ya faru.
Jami’an tsaron sun fafata da ‘yan bindigar ta hanyar musayar wuta, inda suka yi nasarar dakile harin.
An garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibitin da ke kusa domin samun kulawa.
Sai dai likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da mutuwar uku daga cikin wadanda suka jikkata, yayin da sauran 11 ke ci gaba da karbar magani.
Aliyu Abubakar ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Bello Shehu, ya yi Allah-wadai da harin tare da umartar a gudanar da cikakken bincike domin kamo wadanda suka aikata laifin.
NAN













































