Majalisar dattawa ta tabbatar da naɗin Taiwo Oyedele a matsayin minista

Taiwo Oyedele

Majalisar dattawa ta tabbatar da naɗin Taiwo Oyedele a matsayin wanda aka zaɓa domin zama minista a gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu.

Shugaban majalisar dattawa, sanata Godswill Akpabio, ya sanar da tabbatar da naɗin bayan ‘yan majalisar sun amince da shi ta hanyar kaɗa kuri’ar murya a zaman majalisar baki ɗaya.

Ana sa ran Oyedele zai maye gurbin Doris Uzoka-Anite a matsayin karamin ministan kuɗi.

Tabbatar da naɗin tsohon shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan manufofin kasafin kuɗi da gyaran tsarin haraji ya biyo bayan tantancewar da ‘yan majalisar suka yi masa a ranar Laraba.

Sanatoci sun kwashe sama da sa’o’i biyu suna yi masa tambayoyi kafin daga bisani su tabbatar da shi a matsayin wanda aka zaɓa domin zama minista.

A yayin amsa tambayoyin ‘yan majalisar, Oyedele ya bayyana cewa naɗin da aka yi masa a matsayin karamin ministan kuɗi kira ne na yi wa Najeriya hidima.

Ya kuma bayyana cewa yana da fiye da shekaru ashirin yana aiki tare da gwamnatocin ƙasashe, cibiyoyin ƙasa da ƙasa da kuma manyan kamfanonin duniya, inda aikinsa a fannoni masu zaman kansu, ilimi da kuma manufofin gwamnati ya mayar da hankali kan inganta tsarin tafiyar da kuɗaɗen gwamnati da sauya tsarin tattalin arziki.

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ne ya naɗa Oyedele domin maye gurbin Doris Uzoka-Anite, wadda aka sauya mata aiki zuwa karamar ministar kasafin kuɗi da tsare-tsaren ƙasa.

Kwanaki bayan naɗin nasa, shugaban ƙasar ya aika da sunansa zuwa majalisar dattawa domin neman amincewar ‘yan majalisar.

Oyedele ya gode wa shugaban ƙasa Bola Tinubu bisa naɗa shi, inda ya bayyana cewa bayyana gaban majalisar dattawa babban abin girmamawa ne a gare shi.

Kafin wannan naɗin, Oyedele ya yi aiki a matsayin shugaban kwamitin gyaran tsarin haraji, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen samar da sabuwar dokar haraji a Najeriya.

An naɗa shi a wannan mukami a watan Yuli na shekarar 2023, kuma shi da tawagarsa sun shafe sama da shekaru biyu suna gyara dokokin harajin Najeriya.

Duk da cewa a farko an samu suka kan dokokin, daga bisani an fara aiwatar da su a ranar 1 ga watan Janairu, abin da ya nuna fara sabon zamani.

Sabbin dokokin na da nufin sauya tsarin tafiyar da haraji a ƙasar, domin ƙara samun kuɗaɗen shiga, inganta yanayin kasuwanci da kuma ƙara jawo zuba jari daga cikin gida da na ƙasashen waje.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here