Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya naɗa tsohon babban darakta na hukumar kasuwar hada hadar takardun kuɗi da hada-hadar hannayen jari ta Najeriya, Lamido Yuguda, a matsayin mataimakin gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN.
Naɗin, wanda ke jiran amincewar majalisar dattawa, ya fito ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Laraba.
Sanarwar ta bayyana cewa an yi naɗin ne bisa tanadin sashe na 8(1) na dokar Babban Bankin Najeriya ta shekarar 2007.
Onanuga ya ce naɗin Yuguda ya biyo bayan naɗa tsohon mataimakin gwamnan CBN Bala Bello a matsayin mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan tattalin arzikin siyasa.
Sanarwar ta ƙara da cewa shugaban ƙasar ya buƙaci su gudanar da ayyukansu da ƙwazo, ƙwarewa da jajircewa domin tabbatar da daidaiton tattalin arzikin Najeriya da bunƙasarsa a mukaman da aka ba su.
Haka kuma shugaban ƙasar ya buƙaci wanda aka naɗa ya gudanar da aikinsa da ƙwarewa da jajircewa domin tabbatar da daidaiton tattalin arzikin Najeriya da ci gabanta.
Yuguda ya yi aiki a matsayin babban darakta na hukumar SEC daga shekarar 2020 zuwa 2024.
Ya kammala karatu a Jami’ar Ahmadu Bello inda ya samu digirin farko a fannin lissafin kuɗi a shekarar 1983, sannan daga baya ya samu digirin digirgir a fannin kuɗi, harkokin banki da harkokin kuɗi daga Jami’ar Birmingham da ke ƙasar Birtaniya a shekarar 1991.
Shi mamba ne na ƙungiyar kwararrun masu lissafin kuɗi ta Najeriya, sannan kuma ƙwararren mai nazarin harkokin kuɗi ne.
Yuguda ya fara aikinsa a Babban Bankin Najeriya a shekarar 1984 a matsayin babban mai sa ido a sashen harkokin kuɗaɗen waje.
Daga baya ya yi aiki a matsayin masanin tattalin arziki a sashen Afirka na asusun ba da lamuni na duniya daga shekarar 1997 zuwa 2001 kafin ya koma CBN.
Ya yi ritaya daga Babban Bankin Najeriya a shekarar 2016 bayan ya yi aiki a matsayin daraktan sashen kula da ajiyar kuɗaɗe na tsawon shekaru shida.













































