Allah yayi wa fitaccen dan kasuwa, Alhaji Sani Buhari Daura, Walin Daura, rasuwa.
Wata majiya daga danginsa ta shaida wa Solacebase hakan, a ranar Lahadi cewa Walin Daura ya rasu ne a Masarautar Larabawa yana da shekaru 89 a duniya.
Majiyar ta ce ‘yan uwa sun fara shirya gawar mamacin domin yi mata jana’iza.
An haifi marigayi fitaccen dan kasuwan ne a garin Daura a watan Janairun 1932, kuma shi ne mamallakin kamfanin Standard Construction Company Limited.
Akwai Karin bayani anjima…













































