Zargin damfara a shirin tura dalibai karatu ƙasashen waje: hukumar yaƙi da cin hanci ta Kano ta gano asusun Banki 35 da ake zargin mallakar tsohon kwamishina ne

Kano State Public Complaints and Anti graft Corruption Commission PCACC

Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta gano asusun Banki guda 35 da ke da alaƙa da tsohon kwamishinan ilimi mai zurfi, Dr Yusuf Kofar Mata, a cikin binciken da take yi kan zargin damfara a shirin tallafin karatu na ƙasashen waje na jihar.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa a shekarar 2024 wasu manyan jami’an ma’aikatar ilimi mai zurfi ta jihar sun fuskanci tambayoyi kan yadda aka fitar da kuɗaɗe masu yawa a ƙarƙashin shirin ba tare da amincewar gwamna Abba Kabir Yusuf ba.

Bayan gwamnan ya bayar da umarnin gudanar da bincike, an mayar wa gwamnati sama da Naira Miliyan 700 daga cikin kuɗaɗen da aka kashe.

A watan Satumba na shekarar 2024 gwamnan ya amince da ware Naira Biliyan 4.6 domin bai wa ɗalibai 1,001 da ke karatun digiri na biyu tallafin zuwa ƙasashen waje domin ci gaba da karatu.

Daga baya rukuni na farko na ɗaliban ya tafi jami’o’i da ke ƙasashen India, Kenya da Uganda.

Sai dai binciken hukumar yaƙi da cin hanci ya gano cewa ɗalibai 418 ne kawai aka tura ƙasashen waje duk da cewa an fitar da babban kaso na kuɗin da aka ware domin shirin.

Jaridar Solacebase ta samu bayanai a wancan lokaci cewa binciken da ake yi zai gano waɗanda ke da hannu a zargin damfarar tare da tabbatar da an hukunta su bisa doka.

Binciken farko ya nuna cewa an samu wasu ayyukan damfara a ma’aikatar da suka shafi shirin karatu a ƙasashen India da Uganda.

Bayanai da jaridar ta samu a ranar Laraba sun nuna cewa sakamakon binciken da ake ci gaba da yi ya gano cewa tsohon kwamishinan ma’aikatar ilimi mai zurfi ta jihar Kano, Dr Yusuf Ibrahim Kofar Mata, ana zargin yana sarrafa asusun banki guda 35.

An kuma ruwaito cewa tsohon kwamishinan shi ne kaɗai mai sa hannu a asusun banki na kamfanin Crescent Coast Consult and Investment Ltd, wanda aka kafa a watan Afrilu na shekarar 2019, mai ofishin rajista a lamba 24 unguwar Kofar Mata a ƙaramar hukumar Kano birni kuma ana danganta kamfanin da gudanar da aikin sarrafa biza da sayen tikitin jirgi ga ɗaliban da suka samu tallafin karatu na ƙasashen waje na jihar Kano.

Majiyar ta bayyana wa jaridar Solacebase cewa kamfanin ya biya kuɗaɗe na sarrafa biza da sayen tikitin jirgi da suka kai Miliyoyin Naira, abin da ke nuna cewa kamfanin da ake dangantawa da tsohon kwamishinan ya shiga aikin kai tsaye a lokacin da yake riƙe da mukamin kwamishina, lamarin da ke nuna yiwuwar rikicin maslaha.

Lokacin da aka tuntuɓe shi, tsohon kwamishinan ilimi mai zurfi, Dr Yusuf Kofar Mata, ya musanta mallakar asusun banki guda 35 da ake zargin yana sarrafawa.

Ya bayyana cewa wannan lamari ya taso ne saboda ya ƙi shiga jam’iyyar APC.

Duk da tunatar da shi cewa binciken shirin tallafin karatu na ƙasashen waje ya shafe sama da shekara guda yana gudana, Kofar Mata ya dage cewa bai aikata wani laifi ba a duk lokacin da ake aiwatar da shirin.

Ya kuma bayyana cewa kamfanin da aka ambata bai shiga harkar biza da tikitin jirgin ɗaliban ba duk da hujjojin da jaridar ke da su.

Haka kuma jaridar Solacebase ta tuntubi kakakin hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci ta jihar Kano, Isah Mansur Bello, wanda ya tabbatar da cewa gaskiya ne hukumar ta gano asusun banki da dama da ake zargin tsohon kwamishinan, Dr Yusuf Kofar Mata, yana sarrafawa.

Lokacin da aka tambaye shi ko akwai wasu ƙarin abubuwan da aka gano a binciken shirin tallafin karatu na ɗaliban zuwa ƙasashen waje, Bello ya ƙi yin ƙarin bayani, yana mai cewa bincike kan lamarin na ci gaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here