Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da sauran masu ruwa da tsaki na shirin halartar taron masu ruwa da tsaki na aikin Hajji na kasa karo na biyu, wanda zai gudana a Abuja ranar 30 ga watan Afrilu.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mataimakiyar daraktar yada labarai ta hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) Fatima Sanda Usara ta fitar ranar Litinin a Abuja.
Usara ya ce Cibiyar Hajji ta Najeriya (HIN) tare da hadin gwiwar NAHCON, za su gudanar da taron masu ruwa da tsaki na aikin Hajji na kasa karo na biyu da ke da mabanbantan taken, “Dorewar Kudaden Aikin Hajji: Samar da Kyakkyawan yanayi ga Mahajjatan Nijeriya da Ma’aikata”.
A cewarta, ana sa ran mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima zai halarci taron a matsayin bako na musamman yayin da shugaban NAHCON, Farfesa Abdullah Saleh, zai kasance babban mai masaukin baki.
Ta ce a ranar 14 ga Afrilu, an kaddamar da kwamitin gudanarwa na taron, inda Farfesa Wasiu Gabadeen, mataimakin shugaban cibiyar, ya zama shugaba.
“Mambobin kwamitin sun hada da magatakarda na HIN Farfesa Abubakar Ibrahim Jalingo da ma’aikatan NAHCON na sashin tsarin kula da alhazai (HSS) da sauran su.
A cewarta, taron na bana zai mayar da hankali ne kan samar da ingantattun hanyoyin dorewar kudi a matsayin mafarin tunkarar kalubalen kudi da ma’aikatar Hajji ke fuskanta a Najeriya.
Ta ce taron zai kunshi zama hudu ne kowanne ya kunshi wakilai bakwai, wadanda za su jagoranci tattaunawa mai zurfi tare da ba da haske ga kwararru kan batutuwan da suka shafi kudade da gudanar da aikin Hajji. (NAN)













































