Farfesa Adamu Rasheed ya yi ban-kwana da hukumar kula da jami’o’i

0
1688154981140

Farfesa Abubakar Adamu Rasheed a hukumance ya miƙa aiki ga jami’i mafi girman muƙami a hukumar kula da jami’o’i ta Najeriya.

Yayin wani taron miƙa al’amuran hukumar ga Mista Chris Maiyaƙi a Abuja ranar Juma’a, Farfesa Rasheed ya ce ya samu amincewar da ta wajaba ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kafin ya ajiye aiki a yau 30 ga watan Yunin, 2023.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ambato shi yana cewa sabon babban sakatare zai ci gaba da gudanar da harkokin hukuma a matsayin riƙo ya zuwa lokacin da shugaban ƙasa zai naɗa wani jami’i.

‘Saboda burin da nake da shi na shafe tsawon wasu shekaru a aji, na yanke shawarar rubuta wa shugaban ƙasa wasiƙa game da aniyata ta yin murabus ta hanyar ma’aikatar ilmi ta tarayya, shekara uku kafin ƙarewar wa’adina.

”Bayan amincewar ne, na rubuta wa takarda ga Shugaban Jami’ar Bayero Kano don ya ba ni dama na koma aji daga ranar Asabar 1 ga watan Yulin 2023.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here