Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta kayyade Naira miliyan 4.9 a matsayin kudin aikin Hajjin shekarar 2024.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, ta hannun mataimakiyar daraktar hulda da jama’a ta NAHCON, Fatima Sanda Usara.
Idan dai za a iya tunawa hukumar ta kayyade Naira miliyan 4.5 a matsayin kudin ajiya na shekarar duk da cewa maniyyata da dama sun kasa biyan kudaden ajiya.
Sanarwar ta ce an bukaci maniyyatan jihohin Kudu da su biya Naira miliyan 4,899 a matsayin kudin aikin Hajji; Wadanda suka fito daga jihohin Arewa za su biya Naira miliyan 4,699,000, na aikin Hajji, sannan mahajjata daga Yola da cibiyar Maiduguri za su biya Naira miliyan 4,679,000 na aikin Hajjin 2024.
A cewar sanarwar, hukumar ta danganta karuwar kudin da matsalar ke fuskantar tattalin arzikin Najeriya.
Haka kuma hukumar ta bai wa maniyyata aikin hajji zuwa ranar 12 ga watan Fabrairu da su biya kudaden ga hukumar kafin wa’adin ranar 29 ga watan Fabrairu.













































