Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta kama wasu mutum 12 da ake zargi da buga jabun kudi a jihar.
Kakakin rundunar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar ne, ya gabatar da wadanda ake zargin a hedikwatar rundunar da ke jihar.
Ya bayyana cewa sun kama mutanen da ake zargin a garin Bajoga zuwa Dukku a Jihar Gombe.
Ya ce, sun samu rahoton mutanen a ranar 23 ga watan Janairu, 2024 cewar sun damfari wani mai shagon sayar da magani.
Kakakin, ya ce suna samun wannan rahoton suka aike da jami’ansu shagon, inda nan take suka kama daya daga cikin mutanen da jabun kudi.
A cewarsa bayan gudanar da bincike ne suka yi nasarar kama wasu mutum biyar da jabun kudin Dalar Amurka guda 500 da Naira 265,000.
Har wa yau, rundunar ta sake kama wasu mutum shida a garin Malala da ke Karamar Hukumar Dukku da jabun kudi.
Wadanda ake zargin sun amsa laifin da ake tuhumar su da shi, inda suka ce a Jihar Kano suke sayan jabun kudin suke hada su da masu kyau.
Kakakin rundunar ya ce da zarar sun kammala bincike za su tura su zuwa kotu.