
Hukumar kula da hasashen yanayi a Najeriya NiMet ta yi hasashen cewa za’a samu jinkiri wajen saukar ruwan sama a wasu jihohin Najeriya a daminar bana.
NiMet ta ce jihohin akwai Yobe da Jigawa da Sokoto da Kebbi da Kano da Kaduna, kamar yadda jaridar DCL Hausa ta rawaito.
Karanta wannan: Za’a fara hukunta yaran da ba sa zuwa makaranta a Kano – Ma’aikatar Ilimi
Sauran sun hada da Plateau da Nasarawa da Taraba da Gombe da Bauchi da Cross River da tare da Ebonyi da Ogun da kuma Lagos.
Ana hasashen dai a samu jinkirin saukar mamakon ruwan saman a daminar bana a wasu sassan jihohin kasar nan.
Idan dai ba’a manta ba ko a shekarar da ta gabata an samu tsaikon ruwan sama, kafin daga bisani a samu yawaitar mamakon ruwan sama.












































