Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya rasu

Akeredolu
Akeredolu

Kafofin yaɗa labarai a Najeriya na ba da rahotannin cewa Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya rasu.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ce gwamnan ya rasu ne a ƙasar Jamus.

Ya rasu yana da shekara 67, bayan a cewar rahotanni ya shafe lokaci yana fama da cutar kansar jini da kansar mafitsara.

Rasuwar tasa na zuwa ne kimanin mako biyu, bayan Gwamna Akeredolu ya rubuta wasikar tafiya neman lafiya, inda ya miƙa ragamar mulkin jihar ga mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa.

Kafin sannan an yi ta dambarwar siyasa a jihar Ondo, inda ‘yan majalisar jihar suka yi yunƙurin tsige mataimakin daga kujerarsa, amma daga bisani Shugaba Bola Tinubu ya shiga tsakani.

Gwamnan dai ya shafe kusan wata uku a ƙasar Jamus yana jinya, daga bisani ya koma Najeriya a watan Satumba.

An zaɓi Akeredolu a matsayin gwamnan jihar Ondo a wa’adi na biyu a shekara ta 2020.

Ɗan jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, ya fara cin zaɓen gwamna a watan Nuwamban 2016.

An haifi Arakunrin Rotimi Odunayo Akeredolu ranar 21 ga watan Yulin 1956, kuma ya halarci makarantar Aquinas College Akure kafin ya tafi Jami’ar Obafemi Awolowo University da ke Ile Ife.

Ya riƙe muƙamin kwamishinan shari’a na jihar daga 1997 zuwa 1999.

A 1998 ya zama babban lauya mai lambar SAN a Najeriya, sanan ya riƙe shugabancin ƙungiyar lauyoyi ta ƙasar tsawon shekara biyu daga 2008.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here