Mutum 195 ambaliyar ruwa ta kashe a Nijar tare da lalata gida 30,000

FB IMG 16664575736145985
FB IMG 16664575736145985

Ambaliyar ruwa ta yi sanadin mutuwar mutum 195 a Jamhuriyar Nijar tare da shafar mutum 322,000, a cewar alƙaluman da gwamnatin ƙasar ta fitar.

Daminar bana na cikin mafiya muni a tarihi a ƙasashen yankin Afirka ta Yamma.

Haka nan, ruwa ya lalata gidaje fiye da 30,000 kuma ya tagayyara azuzuwa 83, da cibiyoyin lafiya shida, da rumbunan adana amfanin gona 235.

Yankunan da lamarin ya fi shafa su ne Maradi da Zinder da ke tsakiyar ƙasar, da Dosso a kudu maso yamma, da Tahoua a yammaci.

Akan fara ruwa tun daga watan Yuni har zuwa Oktoba, wanda na bana ya fi cin rayukan mutane.

Mutum 70 aka bayar da sanarwar rasuwarsu a 2021 tare da shafar fiye da 200,000. A 2020 kuma, mutum 73 ne suka mutu.

(BBC)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here