Bincike kan gazawar yadda Ake gudanar bangaren kiwon lafiyar jama’a a jihar Neja- M.D. Abubakar

Gov. Sani Bello
Gov. Sani Bello

Jigon kowacce irin gwamnati a kowane mataki shi ne tabbatar da jin dadin ‘yan kasa da kuma kula dasu afannonin samar da ingantacciyar lafiya, mai dorewa da tabbatar da walwar jamaa.

Don haka, abin da ya dace, gwamnatoci a dukkan matakai shine su ba da kulawa ga bangaren kiwon lafiya aƙalla a cikin kasafin kuɗin su. duk da cewa har yanzu anayin kasafi mafi karanci idan aka kwatanta da matakin da majalisar dinkin duniya ta ba da shawara.

Misali, idan aka yi la’akari da kasafi kudi guda biyu da aka yi wa kananan hukumomin kiwon lafiya a jihar Neja kwanan nan, wanda wannan shi ne makasudin wannan rubutu, rahotanni ya nuna cewa an ware sama da Naira Biliyan Goma sha daya ga sashin lafiya a kasafin kudin 2019. yayin da aka ware sama da Naira Biliyan Ashirin a kasafin kudin shekarar 2022, daga cikin jimillar sama da Naira Biliyan Dari da casa’in (shekaru biyu bayan).

La’akari da jihar da ke da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na sama da 1,400 baya ga manyan cibiyoyin kiwon lafiya masu tarin yawa a fadin jihar da ke aiki sama da mutane miliyan hudu bisa ga kidayar 2006 wajibi ne ace an samu sauyi da cigaba.

Har ila yau, ana tsammanin, a waɗannan kasafi ya kamata aga sauyi me kyau da inganci la’akari da makudan kudade da aka lafta dan samun kyakkyawan tsari a asibitoci, kayan aikin likita na zamani da ƙwararrun ma’aikatan kiwon lafiya.

A reshen cibiyar kiwon lafiya na Jummai Babangida na Babban Asibitin Minna, inda matar wani dan uwa na take kwance na tsawon sa’o’i 20 a dakin nakuda, kwatsam aka samu labarin cewa za a yi wa matar sa tiyatar gaggawar Sashin CS amma asibitin ba su da wutar lantarki sakamakon katsewar da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja ya yi a la’akari da irin dimbin bashin da ake bin gwamnatin jihar Neja sama da Naira biliyan daya a tsawon shekaru. Aka kuma sanar da shi cewa asibitin ba shi da man dizwl da za a kunna jannareto ya samar da haske domin gudanar da aikin. Hakan ya sa cikin talatainin dare aka maida su wani asibiti mai zaman kansa da ke Minna, wanda aka cajesu kudin fidar Naira Dubu 200,00. Tabbas ba za ku yi mamaki ko ba mutane bane ko ma dai wasu aljanu ne ke tafiyar da asibitin; ko kuma kawai dai gazawar jami’an gwamnati ne masu kula da harkokin kiwon lafiyar jihar.

Dole ne gwamnati ta mai da hankali kulawa da al’amuran al’umma da suka hada da kiwon lafiya. Har ila yau, dole ne ta ci gaba da horar da ma’aikatanta musamman, wadanda ke cikin dakin fida; wata ruwaya mara dadi ma tace, wata mata unguwar zoma ta zabgawa wata me nakuda mari a lokacin da take kan ga6ar nakudar haihuwa a asibiti, a bisa dalilin irin gurnanin zafin haihuwa da take ji, wannan lamari dole ne ya tunzura duk wani dan Adam mai hankali.

Dole ne jami’an gwamnati su kara himma wajen sanya ido kan ma’aikatansu da kuma sanya takunkumi kan duk wani ma’aikaci da ke nuna rashin da’a da rashin iya aiki. Abubakar ne ya rubuta daga Minna, Jihar Neja kuma za a iya samunsa a muhammadcares4u@gmail.com

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here