Majalisar Ondo ta tabbatar da Aiyedatiwa a matsayin mukaddashin gwamna

Akeredolu and Aiyedatiwa
Akeredolu and Aiyedatiwa

Kakakin majalisar dokokin jihar Ondo, Olamide Oladiji, ya ce ya samu wasika daga gwamna Oluwarotimi Akeredolu kan mika mulki ga mataimakin gwamna Lucky Aiyedatiwa ya zama mukaddashin gwamna.

Sai dai ya ce ana bin tsarin kundin mulki inda zai umarci akawun majalisar domin ya mika amincewar sa ga sakataren gwamnatin jihar.

Akeredolu and Aiyedatiwa

Karanta wannan:Fubara ya gabatar da kasafin kudin jihar Ribas na 2024

Oladiji ya kara da cewa tuni ya sanar da mambobin majalisar a yayin ganawar da suka yi da shugaban kasa Bola Tinubu kuma sun amince da wasikar gwamnan.

A cewar shugaban majalisar, ba za a yi zama a kan lamarin ba domin zai fitar da sanarwa ga manema labarai bayan ya kammala aikin mika mulki ga mataimakin gwamnan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here