Gwamnan jihar Ribas Siminalayi Fubara ya gabatar da naira biliyan 800 a matsayin kasafin kudin 2024, ga majalisar jihar mai mutum biyar.
Wannan na zuwa ne dai-dai lokacin da Ehie ya bayyana kujerun ‘yan majalisu 27 da suka sauya sheka daga PDP zuwa APC a matsayin wadanda ake da gyibin su.

Karanta wannan:Gobara ta kone ofisoshi 17 a Jihar Kano
Har ila yau, an rufe ginin majalisar da safiyar Laraba.
Majalissar ta mutum biyar ta samu jagorancin Edison Ehie wanda a ranar Talatar da ta gabata babbar kotun jihar Ribas ta ayyana shi a matsayin shugaban majalisar.












































