Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce har yanzu ba ta yanke wani hukunci ba dangane da rikicin shugaban kasa da sakatariyar jam’iyyar Labour ta kasa.
Hukumar ta yi wannan karin haske ne a wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na shugaban INEC, Rotimi Oyekanmi, ya fitar ranar Alhamis a Abuja.
Oyekanmi ya kuma ce har yanzu ba ta dau wani mataki a kan sakataren jam’iyyar PDP na kasa ba.
“An ja hankalinmu ga rahotannin da wasu kafafen yada labarai ke cewa hukumar ta amince da wasu mutane a matsayin shugaban jam’iyyar LP na kasa da kuma sakatariyar LP ta kasa.
“Rahotanni sun kuma nuna cewa hukumar ta mayar da wani mutum na musamman a matsayin sakataren jam’iyyar PDP na kasa, dangane da jerin sunayen da ke shafin hukumar.
“Duk da haka, rahotannin karya ne kuma yaudara ce, hukumar ba ta yanke wani hukunci dangane da LP ko PDP ba,” in ji shi.
Oyekanmi ya ce a baya an saka sunayen jami’an LP na kasa a internet na INEC, bisa umarnin kotu, ba tare da wata alaka da sabon hukuncin kotun koli ba.
“Hakazalika, ba a goge sunan sakataren jam’iyyar PDP na kasa a internet ko daya ba, ko kuma a dawo da shi.
“A matsayinta na mai bin doka da oda, hukumar tana nazari sosai kan hukuncin da kotun koli ta yanke kan LP kuma za ta sanar da jama’a hukuncin da ta yanke a kan lokaci,” in ji Oyekanmi. (NAN)