Gwamnatin tarayya ta cire manyan makarantun kasar nan daga tsarin biyan albashi na IPPIS.
Ana sa ran matakin zai fara aiki nan take.
Yanzu haka manyan makarantun za su iya daukar ma’aikata ba tare da kutsen ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya ba.
Karanta wannan:Gobara ta kone ofisoshi 17 a Jihar Kano
Ministan ilimi Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana hakan a karshen zaman majalisar zartarwa na ranar laraba, da ya gudana a Abuja.
Yace wannan wani yunkuri ne na ganin ilimi ya samu kulawar da take bukata tare da kawo karshen kalubalen da fannin ke fuskanta.