ASUU ta Tsawaita Yajin Aikinta da Karin Makwanni Hudu

images 1 5 750x385 1
images 1 5 750x385 1

ASUU ta Tsawaita Yajin Aikinta da Karin Makwanni Hudu.

Kungiyar ta dauki wannan matakin ne a karshen taronta na majalisar zartarwa ta kasa a sakatariyar ta ta kasa da ke Abuja ranar Lahadi.

A wata sanarwa da shugaban kungiyar Farfesa Emmanuel Osodeke ya fitar, kungiyar ta ce.

“Bayan tattaunawa mai zurfi tare da fahimtar gazawar gwamnati a baya wajen cika alkawuranta wajen magance matsalolin da suka taso a cikin yarjejeniyar FGN/ASUU ta 2020 (MOA), NEC ta yanke shawarar kare wa’adin yajin aikin zuwa wasu makonni hudu domin baiwa gwamnati karin lokaci don gamsuwa da warware dukkan batutuwan da suka rage. “Yajin aikin zai fara aiki ne daga karfe 12:01 na safe a ranar Litinin, 1 ga Agusta, 2022.”

Karin bayani na nan tafe..

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here